logo

HAUSA

Xi ya aika sakon ta’aziyya ga takwaransa na Indonesia bisa mummunar girgizar kasar da ta auku

2022-11-22 19:50:54 CMG Hausa

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Indonesia Joko Widodo, dangane da mummunar girgizar kasar da ta auku a kasar.

A cikin sakon nasa, shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kadu matuka da samun labarin cewa, girgizar kasar ta haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi. A madadin gwamnatin kasar Sin da daukacin al’ummar Sinawa, yana mika ta’aziyyar wadanda suka rasu, tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasu da ma wadanda suka jikkata. (Ibrahim)