Kyautata musayar al’adu zai toshe duk wata kafa ta baraka tsakanin Sin da Afrika
2022-11-22 19:44:59 CMG HAUSA
An shiga makon tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya da kuma hadin gwiwa da musayar al’adu tsakanin Sin da Afrika a lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, a jiya Litinin, inda aka yi kira da zurfafa hadin gwiwar bangarorin biyu.
Zan iya cewa kasashen Afrika sun yi dace, inda wannan taro ke gudana jim kadan bayan kammalar taron kolin JKS karo na 20, inda Sin ta saita wata sabuwar akiblar neman ci gaba da zamanantar da kanta.
Dacen da suka yi kuwa shi ne, akwai tarin sabbin darasin da ya kamata su dauka daga sabon tafarkin da Sin ta dauka na raya kanta, baya ga cin gajiyar kudurinta na kara fadada bude kofarta da habaka kasuwanci da kasashen waje.
Wannan taro, kamar sauran tarukan da Sin kan shirya, wata dama ce ga kasashen Afrika ta jan hankalin kamfanonin kasar Sin su zuba jari ko fadada ayyukansu a kasashensu. Kasashen Afrika na da albarkatu da ba a sarrafawa, kasar Sin kuma, na da tarin fasahohi da gogewa a fannin kirkire-kirkire, wanda zai zama hadin gwiwar moriyar juna, da zai kai kasashen Afrika ga amfani da dimbin arzikin da suke da shi, inda za su iya samun ci gaba har ma da kyautata rayuwar jama’a.
Sanin cewa kasar Sin babbar kasuwa ce, ba sabon abu ba ne, don haka fadada kasuwanci da kasar, babbar riba ce. A irin wannan taro ne ya kamata kasashen Afrika su gano abun da ake bukata a kasar Sin kuma su hada gwiwa da kamfanonin kasar domin su taimaka musu fitar da hajojinsu da cin gajiyar babbar kasuwar kasar.
Duniya ta riga ta san yadda Sin take goyon bayan nahiyar Afrika, take kuma kara jan kasashen nahiyar a jiki domin su koyi dabarun raya kansu. Yadda ake kara zurfafa hulda tsakanin bangarorin biyu, na bukatar karin hadin gwiwa da musayar al’adu domin fahimtar juna ta yadda za a toshe duk wata kafa ta baraka a tsakaninsu, ta hakan ne kuma zuri’o’in Sin da Afrika na gaba, za su kasance tamkar ’yan uwa.