logo

HAUSA

Yadda Kasashe Masu Ci Gaba Za Su Cika Alkawuransu Yana Da Muhimmanci Wajen Kare Muhallin Duniyarmu

2022-11-22 13:44:03 CMG Hausa

Bayan mahawarar da aka yi ta tsawon lokaci, a ranar 20 ga wata ne aka rufe taron kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayin ta MDD karo na 27, wato taron COP27 a birnin Sharm el Sheikh na kasar Masar. Yayin taron da aka tsawaita da sa’o’i 36, an zartas da kudurori da dama, kana, daya daga cikinsu wadda ta fi janyo hankulanmu ita ce, amincewa da kafa asusun tallafawa kasashe masu tasowa, da kasashe marasa ci gaba da kudaden yaki da tasirin sauyin yanayi.

Wannan muhimmin sakamako ne da aka cimma, wanda ya amsa bukatun kasashe masu tasowa, wanda zai gaggauta yunkurin fuskantar matsalar sauyin yanayi. A taron na wannan karo, wakilan kasar Sin sun halarci taruka tattaunawa kimanin 100, domin kare moriyar kasashe masu tasowa, inda suka bayar da muhimmiyar gudummawa game da yadda aka cimma sakamako da dama a taron na COP27.

“Duniyarmu tamkar daki ne na masu bukatar jiyyar gaggawa”, kamar yadda babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya bayyana a taron. Akwai wuya gare mu, wajen cimma sakamako mai gamsarwa cikin taron COP27, kuma, akwai ayyuka da dama da za mu yi a nan gaba domin kare muhallin duniyarmu, kana, abin da ya bayar da muhimmanci wajen cimma burinmu shi ne, yadda kasashe masu ci gaba za su cika alkawuransu da kuma sauke nauyin dake wuyansu a wannan fanni. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)