logo

HAUSA

Labarin wani dan kasar Sudan dake karatu a kasar Sin

2022-11-22 16:50:51 CMG Hausa

Masu iya magana kan ce, kasar Sin bangon duniya take, don siffanta tazarar gaske tsakanin Afirka da kasar Sin. A ‘yan shekarun nan, ana kara samun baki ‘yan kasashen waje da suke zuwa kasar Sin don karatu da aiki, ciki har da wasu da suka zabi ci gaba da rayuwa a nan, saboda neman cimma burikansu.

Abdualazem Fadol Mohammed, dan kasar Sudan ne, wanda a yanzu haka yake ci gaba da karatu a cibiyar nazarin ilimin Physics dake kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin, ko kuma The Institute of High Energy Physics of the Chinese Academy of Sciences a turance. A cikin tsawon shekaru sama da hudu da yake karatu a kasar Sin, Abdualazem Fadol Mohammed ya ganewa idanunsa babban ci gaban da kasar ta samu a fannin kimiyya da fasaha. Ba digiri na uku kawai ya samu a kasar Sin ba, har ma ya cimma burinsa na gudanar da bincike a fannin kimiyya da fasaha, al’amarin da ya kai ga ya san sana’ar da zai yi a nan gaba.

“Wannan na’ura ce da ake kira BEPC a Beijing. Idan mun saka kunshin electron cikin wani bututu mai tsawon mita 200, za’a saka wani haske na daban, wanda zai zama positive electron a turance. Daga baya kunshin biyu za su ci karo da juna a cikin na’urar, inda kuma za su amfani juna.”

A cikin dakin gwaji na cibiyar nazarin ilimin Physics dake kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin, Abdualazem Fadol Mohammed, yana bayyana mana yadda na’urorin nan suke aiki. Shi bawan Allah ne mai sha’awar ilimin kimiyya da fasaha, wanda ya iya magana sosai kan batutuwan da suka shafi binciken kimiyya da fasaha.

Malam Abdualazem Fadol Mohammed yana mai cewa:

“Aikin da nake halarta yanzu, aiki ne mai matukar ma’ana. Na fara aiki a nan tun farkon zuwa na kasar Sin, inda muka kafa tawaga, da daukar membobi, da shirya na’urorin aiki.”

Aikin da malam Abdualazem ya ambata, daya ne daga cikin ayyukan da cibiyar nazarin ilimin Physics dake kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin ke halarta tare da sauran wasu kasashe. A shekara ta 2018, Abdualazem ya fara karatun digiri na uku a fannin nazarin ilimin particle physics, da nuclear physics a jami’ar UCAS dake Beijing, wato University of Chinese Academy of Sciences, inda ya kaddamar da aikinsa na nazarin ilimin physics a kasar Sin. A bana, ya kammala karatunsa na digiri na uku, inda kuma zai ci gaba da zurfafa karatunsa a kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin.

Malam Abdualazem ya ce, yana ganewa idanunsa manyan sauye-sauye, gami ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin kimiyya da fasaha. A halin yanzu, yana ci gaba da nazari a wani fannin da ake kira Quantum Computation a turance. Ya ce, kasar Sin na daya daga cikin kasashe kalilan da suke mallakar na’ura mai kwakwalwa da ake kira quantum computer a duniya, al’amarin da ya cancanci babban yabo. Ya kara da cewa, samun damar aikin nazarin kimiyya da fasaha a kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin, abun alfahari ne gare shi, wanda kuma zai amfanar da shi kwarai da gaske. Malam Abdualazem ya ce:

“A halin yanzu, kasar Sin na nazarin samar da na’urori masu kwakwalwa guda biyu da ake kira Quantum Computer. A hakikanin gaskiya, ina amfani da daya daga cikin su wajen gudanar da nazari. Kasar Sin ta shafe shekara da shekaru tana zuba kudade a fannin nazarin kimiyya da fasaha, har ta kai ga samun irin wannan nau’in na’ura mai kwakwalwa mai ci gaba. A kasa ta Sudan, duk da cewa muna da na’urorin nazarin kimiyya, amma akwai sauran rina a kaba gare mu. A gani na, kasa ta za ta koyi dabaru da hikimomin kasar Sin da yawa a wannan fanni.”

A matsayin wani mai nazarin kimiyya da fasaha, malam Abdualazem ya shafe kusan dukkan lokutan sa a fannin aiki, kuma wuraren da ya kan ziyarta a kowace rana sun hada da dakin gwaji, da dakin cin abinci da dakin kwana kawai. Ya ce, rayuwa a kasar Sin na da sauki sosai, musamman a fannonin da suka shafi yin sayayya ta kafar intanet, da biyan kudi ta hanyar amfani da wayar salula, da aikewa da sakwanni, da hawan keken haya da sauransu. Ya ce, kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na shiga cikin kowane fanni na rayuwar mutanen kasar Sin, hakan ba kawai ba shi karin lokaci na aiki da karatu ya yi ba, har ma yana saukaka masa zaman rayuwa na yau da kullum kwarai da gaske.

Mista Abdualazem cewa ya yi:

“Hakika a kasar Sin, za ka iya amfani da wayar salula don yin duk wani abun da kake so. Kafin zuwa na, na saka wasu manhajojin waya na yin hira, kamar wata mai suna WeChat, saboda tana samun karbuwa sosai a kasar Sin. Tun farko ban san mene ne amfaninta ba, sai da na shigo kasar na gano cewa, gaskiya tana da amfani a fannoni da dama, wadda ke kawo sauki sosai ga rayuwarmu ta yau da kullum. A nan, na kuma saka manhajar biyan kudi a waya ta, inda na fara yin sayayya ta kafar intanet, kuma abu na farko da na sayo ta intanet shi ne chess.”

Farkon zuwan sa kasar Sin, malam Abdualazem ya damu sosai saboda bai iya harshen Sinanci ba, amma yanzu yana matukar jin dadin rayuwa a nan, har ma yana shirin gudanar da bikin aure tare da budurwarsa a China, inda za su ziyarci ni’imtattun wuraren yawon shakatawa, da wuraren tarihi tare.

Malam Abdualazem ya bayyana cewa:

“Kasar Sin kyakkyawan waje ne. In ka zo nan ka duba kyan yanayin wajen, za ka fahimci dalilin da ya sa na fadi haka.”

Amma abun da ya fi burge shi shi ne, ya samu damar cimma burinsa na gudanar da aikin nazarin kimiyya da fasaha a kasar Sin. Malam Abdualazem ya ce, yana son zama mai taimakawa inganta mu’amalar Afirka da Sin a fannin kimiyya da fasaha, da taimakawa kwararrun kasar Sudan su zo kasar Sin wajen nazarin kimiyya da fasaha, inda ya ce:

“A fannin kimiyya da fasaha, kasar Sin tana kan gaba a duk fadin duniya. Tana samun ci gaba sosai a wannan fanni. Don haka ya kamata mu yi koyi daga wajen kasar Sin. Ya dace kasashen Afirka su koyi dabaru gami da nasarorin kasar Sin, ta yadda za su samu ci gaba cikin sauri. A nan gaba, ina son zama tamkar manzo tsakanin Afirka da Sin, don inganta samun fahimtar juna da hadin-gwiwa tsakaninsu, kuma ina shirin kafa wata babbar kungiyar kwararrun nazarin kimiyya da fasaha.” (Murtala Zhang)