logo

HAUSA

Xi ya ba da umarni game da hadarin gobarar da ya faru a birnin Anyang na lardin Henan

2022-11-22 19:03:36 CMG Hausa

Da misalin karfe 4 na yammacin jiya ne, wata gobara ta tashi a kamfanin Henan Anyang Kaixinda Trading, kuma ya zuwa yanzu gobarar ta yi sanadiyar mutuwar mutane 38, kana mutane biyu sun jikkata.

Bayan faruwar lamarin, nan take shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayar da muhimmin umarni, inda ya bukaci da a ba da kulawar da ta dace ga wadanda suka jikkata, a kuma kwantar da hankulan iyalansu, a magance matsalolin da suka biyo, tare da gano musababbin hadarin, da kuma yin nazari sosai bisa doka. Haka kuma, a ko wane lokaci ya kamata dukkan yankuna da sassan da abin ya shafa, su kasance masu martaba manufar mayar da jama’a da ma rayuwa a gaban kome, kana su tsaya tsayin daka don hanawa da dakile aukuwar manyan hadurra. (Ibrahim)