logo

HAUSA

Jami’an tsaro sun ceto mutane 76 da aka sace a arewacin Nijeriya

2022-11-22 09:54:28 CMG Hausa

 

Rundunar ’yan sandan Nijeriya, ta ce jami’an tsaro sun ceto matafiya 76 da wasu ’yan bindiga suka sace, yayin da suke tafiya cikin wata babbar mota a kan wani titin jihar Kaduna dake arewacin kasar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya bayyana cikin wata sanarwa a jiya cewa, ’yan sanda sun samu rahoto ranar Juma’a da dare cewa, wasu ’yan bindiga dauke da manyan makamai sun tare wani titin yankin karamar hukumar Giwa ta jihar, domin sace matafiya.

Sanarwar ta ruwaito kakakin na cewa, nan da nan aka hada wani ayarin jami’an tsaro da ya kunshi sojoji da ’yan sanda, kuma da isarsu wurin, sun tarar babu kowa cikin motar. Sai dai bayanan da suka samu, sun nuna cewa ’yan bindigar sun yi awon gaba fasinjoji masu yawa na babbar motar.

Nan take kuma jami’an tsaron suka kaddamar da aikin bincike da ceto cikin dajin dake kusa, lamarin da ya kai su ga cimma ’yan bindigar.

Mohammed Jalige ya ce an ceto mutane 76 da ’yan bindigar suka sace, kuma bayanai daga bincike na farko na cewa, mutanen fasinjoji ne na waccan babbar mota.

Bugu da kari, kakakin ya ce har yanzu jami’an tsaro na sintiri a yankin, inda suke neman direban motar da wasu fasinjoji biyu da ba a gansu ba . (Fa’iza Mustapha)