logo

HAUSA

Sin Na Ingiza Hadin Gwiwa A Ayyukan Ba Da Hidimar Samar Da Bayanai Ta Hanyar Tattara Bayanan Kasa Daga Taurarin Dan Adam

2022-11-22 15:26:43 CMG Hausa

Hukumar lura da ayyukan sama jannati ta kasar Sin ko CNSA, ta ce a jiya Litinin, an kaddamar da wani dandali na kasa, mai samar da hidima a fannin tattara bayanan doron kasa ta amfani da taurarin dan adam, da manhajoji masu nasaba da hakan a birnin Haikou, fadar mulkin lardin Hainan na kudancin kasar.

Kaza lika a cewar CNSAn, ta gudanar da bikin bude dandalin tattara bayanai daga taurarin dan adam na kasa da kasa, da cibiyar hadin gwiwar ba da hidima daga hajoji, da kuma cibiyar BRICS ta ayyukan samar da bayanan doron kasa daga gungun taurarin dan Adam da manhajoji masu nasaba da hakan a Haikou.

Hukumar ta ce tuni kasar Sin ta kaddamar da dandali da zai ba da damar yin musayar cikakken tsarin ba da hidimar bayanan doron kasa daga taurarin dan adam da manhajoji masu nasaba, wanda hakan muhimmin ci gaba ne ga kasar a wannan fanni.

CNSA ta ce cibiyoyin biyu, za su taka rawar gani wajen samar da manufofin samar da bayanai, dake zama fifikon da yankin gabar ruwa na ciniki cikin ’yanci na Hainan ke da shi, da tsara hanyoyin hadin gwiwar kasa da kasa a fannin samar da bayanan doron kasa da manhajoji, da tallafawa wajen aiwatar da hadin gwiwar kasashe karkashin yarjejeniyar lura da yanayin doron kasa, da bunkasa aiwatar da manyan ayyukan kasa da kasa.  (Saminu Alhassan)