logo

HAUSA

Sin da Afirka na yin tasiri mai yakini a duniya

2022-11-22 16:50:55 CMG Hausa

Wasu abubuwa guda 2 da suka faru a kwanan baya sun nuna hadin gwiwar kut da kut da kasashen Afirka da kasar Sin suke yi a fannin kula da harkokin kasa da kasa.

Daya shi ne yadda Afirka da Sin suka hada kai wajen tabbatar da an zartas da kudurin kafa asusun biyan diya ga kasashe masu tasowa, wadanda suka samu hasara sakamakon bala’un da sauyawar yanayin duniya ke haddasawa, a taron bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyawar yanayi ta MDD na COP27, wanda ya kasance wata babbar nasarar da kasashe masu tasowa suka cimma a kokarinsu na muhawara da kasashe masu sukuni.

Dayan kuwa shi ne yadda kasar Sin ta nuna goyon baya ga kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU kan batun halartarta kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G20, inda a wajen taron kolin G20 na 17 da ya kammala a kwanakin baya, kasar Sin ta zama mambar kungiyar G20 ta farko da ta nuna goyon baya ga kungiyar AU a fili.

Na san wadannan abubuwa za su sanya ku yin tambayar cewa, mene ne ya sa har kullum kasashen Afirka da kasar Sin ke hadin kai da juna, yayin da suke kula da al’amuran kasa da kasa?

A gani na, dalili shi ne, kasar Sin da kasashen Afirka suna da tunani iri daya. Da farko, dukkansu na son tabbatar da yanayi na adalci a duniya. Saboda sun taba shan wahala sakamakon tsare-tsaren duniya da kasashen yammacin duniya ke jagoranta, inda a kan yi musu danniya a fannonin siyasa da tattalin arziki. Wannan niyyar bai daya, ta zama wani tushe mai karfi ga hadin gwiwar Sin da Afirka.

Idan mun dauki maganar tinkarar sauyawar yanayin duniya a matsayin misali. Kasashen yamma sun bukaci kasashen Afirka da su dauki nauyin rage fitar da iska mai dumama yanayi iri daya da nasu, ko da yake hakikanin adadin iskar da kasashen Afirka ke fitarwa bai wuce kaso 3 bisa dari na jimillar adadin dukkanin duniya ba. Sai dai a nata bangare, kasar Sin ta jaddada bukatar daukar nauyi mabanbanta tsakanin kasashe masu sukuni da masu tasowa.

Sa’an nan kasar Sin ita ma tana fuskantar matsin lambar da kasashen yamma suke yi mata, inda suke neman soke matsayin kasar na wata kasa mai tasowa, don dora mata matukar nauyi na rage fitar da hayaki da samar da kudi. Duk da haka, kasashen Afirka sun yaba wa kasar Sin kan yadda take kokarin samar da gudunmowa ga aikin raya makamashi masu tsabta a duniya, kana sun bukaci kasashen yamma da su dauki karin nauyi, bisa yadda suka dade suna fitar da dimbin hayaki mai guba cikin shekaru 200 da suka wuce.

Na biyu shi ne, kasashen Afirka da kasar Sin suna dora matukar muhimmanci kan abu daya, wato neman ci gaba. Sabanin yadda wasu kasashen yamma suke dora muhimmanci kan kare ikonsu na yin babakere a duniya, da takara da wasu kasashe, Sin da Afirka na ta kokarin neman hanyar raya kasa. Misali, a taron G20 na wannan karo, kasashen yamma sun fi mai da hankali kan batun dora wa kasar Rasha taken “kasa mai kai hari ga saura”, yayin da a nasu bangare, shugabannin kasashen Afirka da Sin ke nanata kalmomi irinsu “hadin kai”, da “raya kasa”, da “amfanin kowa”, da dai sauransu, a cikin jawaban da suka gabatar.

Ya kamata mu tuna da cewa, yawan al’ummar kasar Sin da ta kasashen Afirka ya kai fiye da kashi 35% na daukacin al’ummar duniya. Duk wadannan mutane masu yawa haka, suna son tabbatar da yanayin adalci a duniya, da kokarin hadin gwiwa don kare moriyar kowa, wannan abun alheri ne ga daukacin ‘yan Adam, wanda ke samar da tasiri mai yakini ga duniyarmu ta wannan zamani. (Bello Wang)