logo

HAUSA

Kamfanin Sinopec na Sin ya kulla yarjejeniyar shekaru 27 da QatarEnergy

2022-11-22 20:37:53 CMG Hausa

Katafaren kamfanin makamashi na Sinopec na kasar Sin, ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar samar da iskar gas (LNG) na tsawon shekaru 27 jiya Litinin. A matsayinsu na kamfanoni mallakar gwamnatocin Sin da kuma Qatar bi da bi, yarjejeniyar za ta baiwa kamfanin QatarEnergy damar samar da tan miliyan hudu na iskar gas a duk shekara ga kamfanin Sinopec. (Ibrahim)