logo

HAUSA

Wakiliyar MDD ta bukaci kasashen yammacin Afirka da su yi amfani da ingantattun dabaru na shawo kan tsattsauran ra’ayi

2022-11-22 09:57:40 CMG Hausa

 

Mai rikon mukamin wakiliyar musamman ta babban magatakardar MDD a yammacin Afirka da yankin Sahel Giovanie Biha, ta yi kira ga kasashen shiyyar yammacin Afirka, da su yi amfani da hadakar ayyukan soji da kyakkyawan jagoranci, domin dakile tsattsauran ra’ayi da ta’addanci a shiyyar.

Giovanie Biha ta yi kiran ne a birnin Accra fadar mulkin kasar Ghana, yayin bikin bude taron ministoci na dandalin Accra. Tana mai cewa aiwatar da hadakar dabarun biyu, zai bunkasa tsare-tsaren cimma nasara a matakin hadin gwiwar daidaikun kasashe, musamman tsakanin ma’aikatu, da hukumomi, da sauran sassa masu alaka da hakan.

Kaza lika Biha ta yi kira ga kasashen yankin, da su karfafa hadin kai domin tinkarar kalubalen raunin wasu kasashe, da karfafa juriya, domin shawo kan manyan kalubalen dake haifar da rashin zaman lafiya da daidaito a shiyyar.

Yayin dandalin, ministan tsaron kasar Ghana Albert Kan-Dapaah, ya ce zaman lafiya da tsaro na ci gaba da zama babban kalubale a yammacin Afirka, inda kuma yanayin ke kara ta’azzara. Amma duk da haka, matakan da ake dauka na da tasirin rage matsalolin, inda karkashinsu ake aiki ta hanyar tattara bayanan sirri, da hadin gwiwar samar da tsaro. (Saminu Alhassan)