logo

HAUSA

Karin sakamakon wasannin gasar cin kofin duniya na Qatar 2022

2022-11-22 10:50:44 CMG Hausa

 

Yayin da ake ci gaba da buga wasannin gasar kwallon kafa na cin kofin duniya, wato FIFA dake gudana yanzu haka a Qatar, a jiya Litinin tawagar kwallon kafar Netherlands ta doke Senegal da ci 2 da nema. Netherlands ta yi nasara ne a wasan rukunin A, bayan ’yan wasan ta Cody Gakpo, da Davy Klaassen sun jefa kwallaye daidai a ragar Senegal. Da wannan sakamako, Netherlands za ta kara da Ecuador a wasan da za a fafata ranar Juma’a, yayin da ita kuma Senegal za ta taka wasa na gaba da Qatar a daidai ranar ta Juma’a. 

A daya wasan kuwa, Ingila ta lallasa Iran da ci 6 da 2, a wasan da shi ne karo na biyu da Ingila ta cimma babban sakamako a tarihin zuwanta gasar cin kofin duniya.

A wasan da aka buga a filin wasa na Ahmed bin Ali, kungiyar Wales ta tashi kunnen doki da Amurka da ci daya da daya a wasan rukunin B. A wasanta na gaba, kungiyar Wales za ta kara da Iran a wasan su na gaba na ranar Juma’a, yayin da Amurka za ta fafata da Ingila a daya wasan na Juma’a.    (Saminu Alhassan)