logo

HAUSA

Sin ta samar da yanayi maras gurbata muhalli a gasar cin kofin duniya na Qatar

2022-11-21 13:40:43 CMG Hausa

A jiya Lahadi 20 ga watan nan ne aka bude gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Qatar. Duk da cewa tawagar kwallon kafar Sin ba za ta buga gasar ba, ana iya ganin alamomin kasar Sin a gasar ta bana, musamman ma fannin manyan ababen more rayuwa da aka gina, ciki har da filin wasa, da aikin samar da ruwa, da na samar da lantarki, wadanda kasar Sin ta taimakawa wajen samar da su.

Babban filin wasa na Lusail mai daukar ’yan kallo 80,000, shi ne mafi girma da za a yi amfani da shi a gasar ta bana, kuma a nan ne za a gudanar da wasanni 10, ciki har da wasan karshe. Kamfanin CRC na kasar Sin ne ya gina filin na Lusail, kuma shi ne filin wasan kwallo na gasar cin kofin duniya na farko da wani kamfannin kasar Sin ya aiwatar da gininsa tun daga tushe, inda kamfanin ya yi nasarar kawar da babakeren kasashe Turai da Amurka a wannan fanni.

Babban sakataren tsare-tsare na gasar ta bana Hassan Al Thawadi ya ce, Qatar ta yi na’am da ingancin ginin filin wasan na Lusail. Filin na da nau’o’in rumfunan ’yan kallo daban daban, kuma kammala ginin sa cikin nasara, shaida ce dake tabbatar da kwarewar aiki ta kamfanonin kasar Sin. (Saminu Alhassan)