logo

HAUSA

An kada kuri’a a babban zaben kasar Equatorial Guinea

2022-11-21 11:04:36 CMG Hausa

Masu zabe a Equatorial Guinea, sun yi tururuwa rumfunan zabe a jiya Lahadi, inda suka fara kada kuri’a a babban zaben kasar na bana, wanda zai ba da damar zaben sabon shugaban kasa, da ’yan majalissar wakilai 100, da kuma ’yan majalissar dattijai 55. Bisa doka, majalissar dattawan kasar na kunshe ne da mambobi 70, amma 15 shugaban kasa ne ke nada su. Kuma ’yan majalissun na aiki ne a tsawon wa’adin shekaru 5.

An dai bude rumfunan zabe ne tun da misalin karshe 8 na safiya, inda aka tsara masu kada kuri’u 400,000 za su jefa kuri’a kafin rufewa da karfe 6 na yamma.

A cewar ofishin watsa labarai na gwamnatin kasar, masu zabe a babban birnin kasar Malabo, sun fara kafa layuka a runfunan zaben tun kusan rabin sa’a kafin lokacin fara kada kuri’un.

Shugaban kasar mai ci Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, mai shekaru 80 a duniya, shi ne dan takarar jam’iyyar PDGE, wanda kuma a wannan karo ke neman sake zarcewa a karo na 6. Cikin manyan masu hamayya da shi kuwa, akwai Buenaventura Monsuy Asumu, na jam’iyyar PCSD, da kuma Andres Esono Ondo na jam’iyyar CPDS.

Zaben ya samu halartar masu sanya ido daga wasu kasashen duniya, da kuma wasu hukumomin kasa da kasa. (Saminu Alhassan)