logo

HAUSA

Kasar Sin ta samu kyawawan sakamako a bangaren kiwon lafiyar al’umma

2022-11-21 11:14:29 CMG Hausa

Mataimakin shugaban hukumar kula da lafiyar al’umma ta kasar Sin, Cao Xuetao, ya ce jarin da Sin ta zuba a bangaren lafiyar al’umma, ya haifar da kyawawan sakamako ba tare da lakume makudan kudi ba.

Cao Xuetao, ya bayyana haka ne yayin taron koli na duniya kan lafiya da aka fara ranar Asabar, inda ya ce matsakaicin tsawon rayuwar al’ummar Sinawa ya kai shekaru 78.2, kuma manyan alkaluman auna ingancin lafiya a kasar sun haura matsakaicin mizanin matsakaita da manyan kasashe ta fannin kudin shiga.

Taron wanda jami’ar Tsingua ta shirya, ya samu halartar kimanin fitattun masana da mambobin hukumomin kasa da kasa kimanin 70 daga kasashe da yankuna 10.

Ya kara da cewa, Kasar Sin za ta ci gaba da shiga ana damawa da ita cikin ayyukan kiwon lafiya a duniya, da aiwatar da shirin raya duniya da hada hannu da sauran kasashe domin yaki da annobar COVID-19, yana mai cewa, kasar za ta kara fadada hadin gwiwa da musaya kan harkokin lafiya da kuma kokarin gina al’ummar duniya mai lafiya ga kowa. (Fa’iza Mustapha)