logo

HAUSA

Xi ya mika sakon taya murna ga taron MDD da Sin kan huldar kasa da kasa game da binciken sararin samaniya

2022-11-21 19:29:06 CMG HAUSA

 

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga taron tattaunawar sabuwar huldar kasa da kasa kan nazarin sararin samaniya da aikin kirkire-kirkire tsakanin MDD da Sin.

A cikin sakonsa, Xi ya yi nuna cewa, a shekarun baya-baya nan, Sin ta himmantu wajen gudanar da ayyukan nazarin sararin samaniya, wadanda suka taimaka wajen habaka ilmin Bil Adama kan sararin samaniya, da kara kawo alheri ga daukacin Bil Adama baki daya. Aikin binciken sararin samaniya ba ya karewa. 

Kasar Sin na fatan kara hada kai da kasa da kasa da habaka mu’ammala da hadin gwiwa, da yin nazari kan sirrikan sararin samaniya tare, da amfani da sararin samaniya cikin lumana, da ingiza bunkasuwar kimiyya da fasahar da za ta amfani al’ummar duniya.

An bude wannan taro ne a birnin Haikou na lardin Hainan. (Amina Xu)