logo

HAUSA

Najeriya tana shirin yin gwanjon rijiyoyin mai da iskar gas guda 7

2022-11-20 16:19:02 CMG HAUSA

 

Hukumar kula da makamashin Najeriya ta sanar da cewa, tana shirin yin gwanjon rijiyoyin mai da iskar gas guda 7 dake karkashin teku nan da karshen wannan wata, karo na farko a cikin shekaru 15.

An ce, wadannan rijiyoyi guda 7 suna cikin ruwa a kusa da yankin ciniki maras shinge na Lekki dake Lagos, sai dai har zuwa yanzu ba a fitar da cikakken bayani game da wadannan rijiyoyin mai da iskar gas guda 7 ba.

A cikin ‘yan shekarun nan, yawan kudin ketare da bangaren makamashin kasar ke samu ya ragu matuka. Alkaluman hukuma sun nuna cewa, a watannin rubu’i na biyu na bana, yawan kudin ketare da aka zuba a fannin man fetur da iskar gas ya ragu da kashi 82%.

Hukumar dake sa ido kan harkokin man fetur na kasar, ta bayyana cewa, a cikin farkon watanni 9 na bana, yawan man fetur da kasar ta hako ya kai kimanin ganga miliyan 332, wanda ya ragu da ganga miliyan 120 bisa na makamancin lokaci na bara, abin da ya sa yawan kudin shiga na gwamanti ya ragu da dalar Amurka kimanin biliyan 12.6.

Hukumar ta bayyana a karshen watan Oktomba cewa, kasar za ta yi gwanjon wadannan wuraren hakar mai da gas. Manazarta na ganin cewa, gwamnatin kasar na fatan samun isassun kudade ta wannan hanya don kara yawan man da ake hakowa a cikin gida ta hanyar gwanjon rijiyoyin mai da iskar gas din.(Amina Xu)