logo

HAUSA

Afirka ta kudu ta yi maraba da sakamakon COP27

2022-11-20 15:49:56 CMG Hausa

Gwamnatin Afirka ta kudu, ta yi na’am da daftarin sakamakon da aka gabatar a yayin taron sassan da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 27 ko COP 27 a takaice jiya Asabar.

An dai gudanar da taron COP27 ne a kasar Masar, daga ranar 6 zuwa 18 ga watan Nuwamban shekarar 2022 da muke ciki. Gwamnatin Afirka ta kudu ta bayyana cewa, ta fahimci abubuwa da dama da aka tattauna yayin taron, ciki har da yadda sauyin yanayi ke karuwa cikin gaggawa.

Mai magana da yawun sashen kula da muhalli da gandun daji da kamun kifi na kasar Peter Mbelengwa, ya bayyana cewa, daftarin ya zayyana matsalar sauyin yanayi da hanyoyin magance ta dangane da manufofin ci gaba mai dorewa da matakai kawai, ba tare da barin kowa a baya ba, da bukatar yin gyaran fuska a bangarorin hada-hadar kudade don cimma wadannan manufofi.

Mbelengwa ya bayyana cewa, kasarsa na san bankunan ci gaban sassa daban-daban da cibiyoyin kudi na kasa da kasa, za su dauki kwararan matakai, don inganta harkokin kudaden magance matsalar sauyin yanayi a shekara 2023, da fito da tsare-tsare da suka shafi hukumominsu yadda ya kamata. (Ibrahim)