logo

HAUSA

MDD ta damu da tashin hankalin dake faruwa a Sudan ta kudu

2022-11-20 15:36:39 CMG Hausa

Tawagar MDD dake aikin tabbatar da zaman lafiya a Sudan ta kudu (UNMISS) ta bayyana cewa, ta damu ainun kan tashin hankalin dake faruwa a jihar Upper Nile na kasar Sudan ta kudu.

A cewar tawagar ta UNMISS, fadan da ake gwabzawa a yankin Fashoda, tsakanin matasan Shilluk masu dauke da makamai da ‘yan kabilar Nuer, na yin tasiri kan rayuwar fararen hula da dama, inda rahotanni ke cewa, mutane da dama na kaura zuwa garuruwan Malakal da Kodok, inda lamarin ke ci gaba da kara tabarbarewa.

Wata sanarwa da tawagar ta fitar a Juba, babban birnin kasar na cewa, tashe-tashen hankula da ake samu tsakanin kungiyoyi daban-daban da suka fara a wadannan yankuna a cikin watan Agustan shekarar 2022, sun yi sanadin raba dubban mutane da muhallansu, baya ga cin zarafi da kashe wasu da lalata dukiyoyi.

Don haka, tawagar ta UNMISS ke kira ga mahukunta, da manyan jagororin al’umma, da dattawa daga kungiyoyin Shilluk da Nuer, na jihohin Jonglei da Upper Nile, da su yi amfani da matsayinsu wajen dakatar da tashe-tashen hankulan da hana ci gaba da cin zarafin fararen hula.(Ibrahim)