logo

HAUSA

Wang Yi: Ziyarar Xi a ketare na nuni da yadda Sin ta himmatu wajen samun ci gaban duniya

2022-11-20 15:23:36 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana cewa, halartar taron kolin G20 karo na 17, da taron shugabannin hadin gwiwar tattalin arziki na kasashen yankin Asiya da tekun Fasifik karo na 29, da kuma ziyarar aikin da ya kai kasar Thailand, na nuni da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya, da kara bude kofa da yin hadin gwiwa.

Wang ya shaidawa manema labarai cewa, sanin kowa ne cewa, a cikin gida da kuma waje a gabar da duniya ake fuskantar wani yanayi mai sarkakiya, ta hanyar sa kaimi ga bunkasuwar duniya da tafiyar da harkokin kasa da kasa, kasar Sin ta nuna rawar da take takawa a matsayinta na babbar kasa.

Ya jaddada cewa, yayin ziyarar da ya kai ta kwanaki 6, shugaba Xi ya halarci ayyuka fiye da guda 30, da kokarin ganin an raya da jagorancin tafiyar da harkoki na duniya, da nuna matsayin kasar Sin a matsayin babbar kasa mai rikon amana da sanin ya kamata.

A yayin da yake jawabi ga taruka masu nasaba da bangarori daban-daban da dama da kuma tattaunawa da shugabannin wasu kasashe kuwa, shugaba Xi ya yi karin haske kan sakamakon babban taron wakilan JKS karo na 20 da ya kammala cikin nasara, da batun zamanantar da kasar Sin, da hadin gwiwar samun nasara tare tsakanin Sin da ragowar kasashen duniya.

Wang ya kara da cewa, ana sa ran kasar Sin za ta samu ci gaba mai inganci da bude kofa ga kasashen ketare. Yana mai nuni da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da inganta zaman lafiya da ci gaban duiya, da zurfafa bude kofa da yin hadin gwiwa da ragowar kasashen duniya. (Ibrahim)