Sin ta nuna alhakin dake wuyanta a matsayinta na babbar kasa
2022-11-20 20:35:27 CMG Hausa
Jiya ne, aka kammala taron shugabannin kungiyar kasashen yankin Asiya da Fasifik (APEC) karo na 29 a kasar Thailand. Taron ya zartas da muhimman takardun sakamako guda biyu, da sanarwar shugabannin APEC, da burin Bangkok na raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, wanda ke nuna manufofi da shawarwari da suka dace da kasar Sin.
Kafofin watsa labarai na kasa da kasa sun yi imanin cewa, muhimmin jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ya kara haskaka “lokacin yankin Asiya” na tafiyar da harkokin duniya, kuma kasar Sin ta kasance jagora wajen hada kan dukkan sassa don tunkarar kalubaloli iri daya.(Ibrahim)