logo

HAUSA

Sin ta kafa sabon bajinta a fannin kara ingancin batir ta silicon mai amfani da hasken rana

2022-11-20 16:20:35 CMG HAUSA

 

Cibiyar nazarin makamashin hasken rana ta kasar Jamus (ISFH) ta ba da sabon rahoto cewa, batirin silicon mai amfani da hasken rana da kamfanin Sin ya kirkiro, yana iya juya hasken rana zuwa wutar lantarki da kashi 26.81%, wanda ya kasance matsayin koli a duniya a wannan fanni.

An ba labari cewa, jigon ci gaban fasahar amfani da karfin hasken rana shi ne inganta aiki na juya karfin hasken rana zuwa wutar lantarki da rage farashin wutar lantarki. Batir din da Sin ta kirkiro a wannan karo yana da ingancin aiki matuka.

Rahotanni na cewa, kasar Sin ta kafa wannan bajimta ne bisa batir din dake iya amfani da hasken rana wajen samar da wutar lantarki na kashi 26.7 da kasar Japan ta kirkiro a shekarar 2017, shekaru 5 da suka gabata, Sin ta kafa wani sabon bajimta, kuma shi ne karon farko da kamfanin Sin ya kafa bajimta a wannan fanni. (Amina Xu)