logo

HAUSA

Xi Jinping ya ci gaba da halartar taron karba-karba na shugabannin mambobin kungiyar APEC karo na 29

2022-11-19 16:54:41 CMG Hausa

A yau da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ci gaba da halartar taron karba-karba na shugabannin mambobin kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Pasifik APEC karo na 29 a birnin Bangkok dake kasar Thailand, inda aka tattauna kan batutuwan cinikayya mai dorewa da zuba jari.

Shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, yin ciniki da zuba jari cikin ‘yanci da bude kofa, ka’ida ce ta kungiyar APEC, kana shi ne jigon cimma burin Putrajaya na shekarar 2040.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kamata a tsaya kan manufar cudanyar sassa daban daban, da tabbatar da tsarin yin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, da hakuri da bambance-bambance tsakanin bangarori daban daban don samun moriyar juna, da kuma kiyaye bude kofa a yankuna don samun wadata a yankin Asiya da tekun Pasifik. Ya kara da cewa, kasar Sin ba za ta canja ra’ayinta na bude kofa ga kasashen waje ba, kana za ta kara aiwatar da irin wannan manufa. Haka kuma, Sin za ta fadada shigo da kayayyaki da hidimomi masu inganci zuwa kasar, don kara samar wa duniya damar yin kasuwanci, da samun bunkasuwa, da kuma hadin gwiwa.

A yayin taron, an gabatar da sanarwar shugabannin kungiyar APEC ta shekarar 2022, da kuma manufar Bangkok kan raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba. (Zainab)