logo

HAUSA

Peng Liyuan Ta Ziyarci Kwalejin Nazarin Kide-Kide Na Princess Galyani Vadana

2022-11-19 20:45:35 CMG Hausa

Uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan, tare da Naraporn Chan-ocha, uwargidan Firaministan kasar Thailand, sun ziyarci kwalejin nazarin kide-kide na Princess Galyani Vadhana ta kasar Thailand.

Yayin ziyarar, Peng Liyuan tare da Naraporn Chan-ocha, sun saurari tarihin kwalejin da hadin gwiwarta da kasashen waje, haka kuma sun yi farin ciki da kulla hadin gwiwa tsakanin kwalejin da jami’ar fasaha ta Nanjing ta kasar Sin.

Har ila yau, Peng Liyuan ta bayar da kyautar Guzeng, wani kayan kida na gargajiya na kasar Sin da littattafai kan kide-kide da al’adun Sin da wasu kayayyakin bidiyo da na murya, tana fatan matasan kasar Thailand za su koyi amfani da kayayyakin kide na kasar Sin da kuma musayar al’adu tsakanin kasashen biyu. (Fa’iza)