logo

HAUSA

Xi Ya Gana Da Mataimakiyar Shugban Amurka

2022-11-19 15:52:09 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana a yau Asabar cewa, yana fatan kasashen Sin da Amurka za su kara kyautata fahimtar juna domin kaucewa bahaguwar fahimta da kuma hada hannu domin mayar da dangantakarsu bisa turbar da ta dace.

Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin wata gajeriyar ganawa da ya yi da mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris, a gefen taron kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Pasifik karo na 29.

Da ya yi waiwaye kan ganawarsa da shugaba Joe Biden na Amurka a tsibirin Bali na kasar Indonesia, shugaba Xi ya ce tattaunawarsu, ta na da muhimmanci wajen jagorantar dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon babi. Kuma yana fatan mataimakiyar shugaban za ta taka rawa wajen tabbatar da hakan.

A nata bangare, Kamala Harris ta ce shugabannin biyu sun gana cikin nasara, kuma Amurka ba ta neman yin fito na fito ko rikici da Sin, kuma ya kamata bangarorin biyu su hada hannu kan batutuwan da suka shafi duniya da bude kafofin tuntubar juna. (Fa’iza Mustapha)