logo

HAUSA

An shiga mataki na 5 na gangamin allurar rigakafin COVID-19 a Kamaru

2022-11-19 16:24:15 CMG Hausa

 

Ma’aikatar kula da lafiyar al’umma ta Kamaru, ta ce an shiga mataki na 5, na gangamin allurar rigakafin cutar COVID-19 a kasar, a jiya Juma’a.

Gangamin wanda zai shafe tsawon kwanaki 10, zai mayar da hankali ne kan mutane masu shekaru 18 zuwa sama, da mutanen da suka cancanci karbar rigakafin karo na 3 domin karfafa garkuwar jiki, da mata masu juna biyu da kuma masu shayarwa.

Wani masanin kiwon lafiyar al’umma a kasar, James Ndefru, ya shaidawa kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, hukumomi na kara kaimi wajen wayar da kan al’umma domin tabbatar da kowa ya karbi rigakafin.

Ministan kula da lafiyar al’umma na kasar Manaouda Malachie, ya bayyana a watan da ya gabata cewa, a matsayin wani bangare na tunkarar cutar COVID-19, Kamaru ta riga ta yi wa kaso 12 na al’ummarta masu shekaru 18 zuwa sama rigakafin, inda zuwa yanzu, sama da mutane miliyan 1.8 suka karba.

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika, ta ce tun bayan watan Maris na shekarar 2020, Kamaru ta fara yaki da cutar, inda kawo yanzu aka tabbatar da mutane 123,993 sun kamu. (Fa’iza Mustapha)