logo

HAUSA

Sin Da Thailand Sun Amince Da Gina Al’umma Mai Makoma Ta Bai Daya

2022-11-19 20:43:48 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da Firaministan kasar Thailand Prayut Chan-o-cha, sun amince da gina al’umma mai makoma ta bai daya ta Sin da Thailand mai karfi da ci gaba da kuma dorewa.

Wannan na kunshe ne cikin sanarwar hadin gwiwa da aka fitar bayan ganawar shugabannin biyu a yau Asabar. (Fa’iza)