logo

HAUSA

Zhang Weili ta karbe kambin UFC ajin marasa nauyi

2022-11-18 15:25:48 CMG Hausa

‘Yar wasan damben kasar Sin Zhang Weili, ta haye saman teburin gasar “UFC 281 card”ajin mata marasa nauyi, yayin karawar ta da wadda ke rike da kambin gasar karo 2 a jere wato Carla Esparza. Yanzu haka dai Zhang ta karbo kambin ta wanda a baya ta taba lashewa. A ajin maza kuwa na gasar da hukumar UFC ke shiryawa, Alex Periera ya doke abokin karawarsa king Israel Adesanya, a gasar ajin masu matsakaitan nauyi.

Yayin fafatawar Zhang da Esparza, Zhang din ce ta mamaye zagayen farko na wasan. Duk da Esparza ta yi iya kokari na lashe fafatawar. Sai dai daga karshe, Zhang wadda ta mamaye wasan ta ci gaba da kare matsayin ta a damben mai hade da kokawa, har ta kai ga ganin karshen kwazon ‘yar wasan Amurka a filin wasa na Madison Square dake birnin New York.

An ci gaba da fafata sauran zagayen damben har zuwa karshen wasan, Esparza ta yi iya yin ta amma Zhang ta yi amfani da kwarewar ta a salon jiujitsu, domin dakile abokiyar karawar ta har karshe.

Bayan kammala wasan, ‘yar dambe Zhang ta bayyana cewa, "Ina da dabaru masu yawa na kammala wannan wasa, ta yin kwantan-bauna ga abokiyar karawa ta daya ne daga dabaru na”.

A cewar Zhang, wadda ta zama da ‘yar dambe ta 3 a tarihi da ta taba kwato kambin ta, bayan da a baya ta fuskanci rashin nasara a ajin ‘yan wasa marasa nauyi, ta ce "A yau buri na ya cika, na kuma kwato kambi na. Ina godewa magoya baya na na Sin da Amurka, da ma duniya baki daya".

Zhang ta zamo ‘yar dambe mai hade da kokawa ta farko daga Asiya, da ta lashe gasar UFC a shekarar 2019. Daga baya kuma a shekarar 2021, ta yi rashin nasara a hannun Rose Namajunas, kaza lika Zhang ta ci gaba da kokarin kwato wannan kambi, inda a watan Yunin bana ta yi nasara kan Joanna Jedrzejczyk.

A wasan karshen makon nan, dubban magoya bayan Zhang sun rika Shewa da murnar nasarar da ta cimma, ciki har da masoyanta da suka halarci wasan daga nisan duniya. Da yawa daga cikin su sun bayyana matukar gamsuwa da kwarewar da Zhang ta nuna a wasan na baya bayan nan.

Wata Baamurkiya mai suna Ashton daga jihar North Carolina ta Amurka, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa "Zhang ta nuna karfin jiki da kwarewar fasahohi, shi yasa nake jiran sake kallon fadan ta". Ashton wadda ta halarci wasan tare da mahaifin ta Michael Kerekes, ta kara da cewa, "ban jima da sanin ta ba. Ta nuna karfin hali da karfin jiki sosai". Shi ma Mr. Michael ya ce ya san cewa, Zhang za ta yi nasara tun ma kafin a fafata wasan. Ya ce "Tana da kwarewa sosai ta ko wane bangare sama da Carla. Na san cewa lokacin da suke kokawa a kasa tana da karfin jure fafatawar duk rintsi. Kuma a yayin da suke dambe a tsaye, tana da juriya da karfi sama da Carla. Don haka na san za ta yi nasara a wannan wasa."

Ya ce "Yayin da Carla ke gwada kwarewa a kokawar kasa, Zhang ta san me za ta yi. Don haka ta nuna mata fin-karfi, ta rika juya bangarorin jikin ta da kwarewa, har ta kai ga yin nasara a karshen wasa."

Shi ma yayin tattaunawa da Xinhua, wani mai sha’awar wasan dambe da ya shafe shekaru kusan 5 a birnin New York mai suna Chen Ziran, ya isa wurin wasan da tutar kasar Sin. Ya kuma bayyana cewa "Na jima ina kaunar wasan dambe da UFC ke shiryawa, kuma tabbas ina kaunar Weili, wannan ne ya sa na zo nan domin nuna mata goyon baya”.

Ita kan ta Zhang ta bayyana cewa “Na rika samun karin karfin gwiwa, ganin tutar kasar Sin a wani wuri da nake wasa nesa daga gida”.

A ajin maza na gasar ta UFC kuwa, ‘yan dambe 2 na ajin matsakaicin nauyi, sun fafata a wasan su na karshe, bayan da a baya suka taba fafatawa, a kuma wannan karo ma Alex Periera daga Brazil ne ya yi nasara kan abokin karawarsa king Israel Adesanya dan Najeriya da New Zealand.