logo

HAUSA

Shawarwari 4 Na Kasar Sin Za Su Taimaka Wajen Samar Da Sabon Abun Al’ajabi A Asiya Da Yankin Tekun Pasifik

2022-11-18 21:18:52 CMG Hausa

Ranar 18 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana cikin jawabinsa a yayin kwarya-kwaryar taron shugabanni mambobin kungiyar hadin kan tattalin arziki ta Asiya da yankin tekun Pasifik APEC karo na 29 cewa, yanzu duniya ta sake shiga muhimmin lokaci a tarihi. Asiya da yankin tekun Pasifik suna kara taka muhimmiyar rawa, yayin da matsayinsu ya samu ingantuwa sosai.

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda 4 kan yadda za a hada hannu wajen raya makomar bai daya a Asiya da yankin tekun Pasifik a sabon halin da ake ciki, wato kiyaye adalci a duniya, a kokarin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Asiya da yankin tekun Pasifik, da tsayawa kan bude kofa ga ketare da dunkule dukkan bangarori, a kokarin raya Asiya da yankin tekun Pasifik mai wadata, da nacewa kan raya Asiya da yankin tekun Pasifik mai tsabta da kyan gani ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma tsayawa kan taimakawa juna a Asiya da yankin tekun Pasifik, wadanda ke da makoma iri daya.

Ruhin wadannan shawarwari 4 sun yi daidai da shawarwari guda 6 da Xi Jinping ya ambato cikin rubutaccen jawabinsa a yayin taron shugabannin masana’antu da kasuwanci na kungiyar APEC a ranar 17 ga wata. Dukkansu sun takaita fasahohin da aka samu wajen samar da abun al’ajabi na Asiya da yankin tekun Pasifik, sun kuma tsara manyan tsare-tsare kan halin da ake ciki yanzu. Shawarwarin na da ma’ana mai zurfi kan hakikanin halin da ake ciki.

Ba za a samu ci gaba ba, sai an samu zaman lafiya tukuna. Kana kuma, ci gaba ya na ba da tabbaci wajen samun zaman lafiya. A matsayinta na muhimmiyar mambar kungiyar APEC, kasar Sin ta samu ci gaba sakamakon kasancewa a Asiya da yankin tekun Pasifik, yayin da ta ba da nata gudummowa wajen raya Asiya da yankin tekun Pasifik. Ya zuwa shekarar 2020, jimillar yawan cinikin da ke tsakanin Sin da mambobin kungiyar APEC ta kai dalar Amurka triliyan 2.87. Kwanan baya, an samu nasarar gwajin layin dogon Jakarta-Bandung mai saurin tafiya. An fara aiki da tasoshin dakon kaya a layin dogo tsakanin kasar Sin da kasar Laos. Kana an fara amfani da babban titin dake tsakanin Phnom Penh da tashar jiragen ruwa ta Sihanoukville a kasar Cambodiya. Lalle ayyukan raya ababen more rayuwar jama’a karkashin inuwar shawarar “ziri daya da hanya daya”, sun kyautata hadewar sassa daban daban a Asiya da yankin tekun Pasifik. Kasar Sin za ta ci gaba da daukar hakikanin matakai don nuna yadda take aza harsashi a Asiya da yankin tekun Pasifik, da raya yankin da kuma kawo alheri ga yankin. (Tasallah Yuan)