logo

HAUSA

Za a gudanar da dandanlin tattaunawar Zhongguancun 2022 daga ranar 25 zuwa 30 ga watan Nuwamba

2022-11-18 15:28:46 CMG Hausa

Za a gudanar da taron dandanlin tattaunawar Zhongguancun na shekarar 2022 a birnin Beijing daga ranar 25 zuwa 30 ga watan Nuwamba. Jigon dandalin tattaunawar na wannan karo shi ne “yin hadin gwiwa tare da bude kofa, tare da cin gajiyar makoma tare”. Za a yi wannan taron dandalin tattaunawa ne a Cibiyar taro ta kasa ta Beijing. A sa’i daya kuma za a gudanar da ayyuka guda 126 a cikin cibiyar baje koli ta yankin ba da misalai na kirkira na Zhongguancun da wurin bude ido na Shougang. (Safiyah Ma)