logo

HAUSA

Najeriya: Zazzabin Lassa ya hallaka mutane 177

2022-11-18 10:52:50 CMG Hausa

Cibiyar kandagarki da yaki da cututtuka ta Najeriya ko NCDC, ta ce a shekarar bana, adadin mutanen da cutar zazzabin Lassa ta hallaka ya karu zuwa 177, a gabar da gwamnatin kasar ke kara azamar rage yaduwar cutar.

Mahukunta a cibiyar ta NCDC sun ce daga farkon shekarar nan zuwa yanzu, an samu tabbacin harbuwar jimillar mutane 975 da cutar a jihohin kasar 26. Kaza lika a tsakanin ranakun 31 ga Oktoba zuwa 6 ga watan Nuwamban nan kadai, an samu sabbin mutane da suka harbu da cutar su 17.

Da wannan sabon adadi, NCDC ta ce mizanin hadarin mace-mace daga cutar ya karu zuwa kaso 18.2 bisa dari. Bugu da kari, matsakaicin shekarun wadanda cutar ta fi shafa su ne ’yan shekaru 21 zuwa 30, wanda ya kunshi kaso 10 na maza da kaso 8 na mata. (Saminu Alhasan)