logo

HAUSA

Ministan tsaron Ghana ya bukaci hadin gwiwa don yaki da tsattsauran ra'ayi da ayyukan ta'addanci a yammacin Afirka

2022-11-18 09:58:32 CMG Hausa

Ministan tsaron kasar Ghana Albert Kan-Dappah, ya bukaci kasashen Afirka da su gaggauta hadin gwiwa a tsakaninsu, domin yaki da kuma shawo kan tagwayen barazanar tashin hankali da ayyukan ta'addanci a yammacin Afirka.

Ministan ya yi wannan kiran ne a jawabinsa na musamman da ya gabatar, a yayin bude taron masu zaman kansu na yini biyu game da shirin Accra, shirin hadin gwiwa kan inganta matakan tsaro tsakanin wasu kasashen yammacin Afirka.

Ya kara da cewa, game da batun tsaro, yankin Sahel da daukacin yammacin Afirka, na cikin wani mawuyacin hali da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi, sakamakon yadda ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi ke ci gaba da yaduwa cikin sauri.

Ya bayyana cewa, dabarun yankin game da yaki da ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi, da tasirinsa kai tsaye kan dorewar yankin, suna ci gaba da canzawa ba tare da gargadi ba. A hannu guda kuma barazanar da COVID-19 ke haifarwa ya nuna cewa, kara kaimi a matakin yanki, shi ne hanya mafi dacewa, na tabbatar da tsaron kasashen yankin.

Kan-Dapaah ya ce, tattaunawa da mu’amala tsakanin masu ruwa da tsaki a matakin kasa da na shiyya, na da matukar muhimmanci, wajen samar da mafita mai dorewa kan barazanar tsaro da kasashen yammacin Afirka ke fuskanta. (Ibrahim)