logo

HAUSA

Sin Na Ba Da Gudunmar Ci Gaban Duniya

2022-11-18 15:17:26 CMG HAUSA

Daga MINA

Abokai, yayin da ‘yan kwanaki suka rage a fara gasar cin kofin kwallon kafan duniya ta hukumar FIFA ta 2022 a Qatar, yau “duniya a zanen MINA” zai bayyana muku abubuwan dake da alaka da kasar Sin a wannan gasa da ma duniya.

Yayin da ka yi yawo a wajen filin wasa na Al Bayt , abin da zai shakatar da kai a filin, shi ne wasu bishiyoyi masu kyaun gani na kudancin kasar Sin da yawansu ya kai fiye da dubu 50, da kamfanin samar da tsirrai na birnin Foshan na lardin Guangdong dake kudancin Sin ya yi jigilarsu zuwa wurin. Ban da wannan kuma, sama da kashi 50% na kayayyakin dake da alaka da gasar daga birnin Yiwu na Sin ne aka samar, baya ga rigunan wasa na fitattun kungiyoyin ‘yan wasa na kasashe 32 da mai tsara salon tufa na Sin ya gabatar da mutum zai iya saya. Haka kuma, kamfanin Sin ne ya gina filin wasa na Lusail, daya daga cikin filaye mafiya kayatarwa da muhimmanci na gasar.

Bayan ga wadannan abubuwa da Sin ta samar a gasar, yanzu haka kayayyakin da Sin ta samar da manyan ababen more rayuwa da Sin ta gina sun karade sassa na duniya. Idan muka juya ga nahiyar Afrika kuwa, daga layin dogo tsakanin Tanzaniya da Zambiya zuwa layin dogo dake tsakanin Abuja da Kaduna, daga madatsar ruwa ta Merowe zuwa tashar jirgin ruwa mai zurfi ta Lekki ta ciniki cikin ‘yanci, da ma wasu abubuwa na yau da kullum, dukkansu Sin ce ta gina su. Tambayar ita ce, wai me ya sa kasar Sin ta gina wadannan abubuwa masu tarin yawa a duniya?

Bayan shekaru fiye da 40 da Sin ta fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, Sin ta zama kasa mai karfi a fannin masana’antu a duniya. Ban da wannan kuma, a cikin tsarin zamanintar da masana’antu da Sin ta gudanar, gwamnati ta mai da hankali matuka kan kimiyya da fasaha. Alal misali, layin dogo da kamfanin Sin ya shimfida a cikin Abuja, shi ne irinsa na farko a yammancin Afrika dake amfani da tsarin kasar Sin. Ban da wannan kuma, fasahar sadarwa ta 5G da manyan ababen dangane da hakan da ake amfani da su yanzu a Afrika, su ma kamfanonin Sin suka gina su.

Sanin kowa ne cewa, ana yabawa kayayyakin da Sin ta samar saboda inganci da kuma araha, baya ga haka, abubuwan da Sin ta samar ta hanyar kirkire-kirkire bisa fasaha da kimiyya, sun fara jawo hankalin duniya. Kasashe daban-daban na sa ran shigo da kayayyakin Sin cikin kasashensu da kuma hada kai da kamfanonin Sin a fannin samar da kayayyaki da fasaha da kimiyya, kazalika suna zabar kamfanonin Sin, don su taimaka musu wajen gina wasu manyan ababen more rayuwa. A nata bangare, Sin tana matukar fari ciki wajen hada kai da kasashen duniya musamman ma kasashe masu tasowa don samun moriya tare.(Mai zane da rubuta:MINA)