logo

HAUSA

Xi ya gana da shugabannin wasu kasashe

2022-11-18 10:50:36 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, a shirye kasarsa take ta yi aiki tare da kasar Japan, don kiyaye dangantakar dake tsakanin kasashen biyu kan turbar da ta dace bisa manyan tsare-tsare, da kulla huldar dake tsakanin Sin da Japan da ta dace da sabon zamani

Xi ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da firaministan Japan Fumio Kishida a gefen taron shugabannin hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da tekun Fasifik wato APEC karo na 29.

A nasa jawabin, Firaminista Kishida ya bayyana cewa, da kyar kasar Japan za ta iya samun ci gaba da wadata ba tare da kasar Sin ba, haka ma lamarin yake ga bangaren kasar Sin.

A lokacin da yake ganawa da takwaransa na kasar Philippines Ferdinand Romualdez Marcos kuwa, shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin tana kallon dangantakarta da Philippines bisa manyan tsare-tsare.

A nasa bangaren, shugaba Marcos ya sake mika sakonsa na taya murnar kammala babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 cikin nasara, da kuma sake zaben Xi a matsayin babban sakataren kwamitin kolin JKS. Yana mai cewa, hakan ya kawo kwanciyar hankali ba kawai ga ci gaban kasar Sin a nan gaba ba, har ma da yankin da ma duniya baki daya.

A yayin ganawarsa da firaministan kasar Singapore Lee Hsien Loong, Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin tana maraba da yadda kasar Singapore ke kokarin gina sabon tsarin raya kasa, kuma ya kamata a ce " inganci mai kyau" ya kasance alamar hadin gwiwa tsakanin Sin da Singapore.

A nasa bangare, firaminista Lee ya ce, kasar Sin mai karfi da abokantaka, za ta kawo kyakkyawan tasiri ga yankin da ma duniya baki daya, kuma za ta taimakawa kanana da matsakaitan kasashe wajen samun ci gaba tare. (Ibrahim)