logo

HAUSA

Xi Jinping ya gabatar da jawabi yayin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 29

2022-11-18 15:25:06 CMG Hausa

Shugaban Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi yayin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 29 a yau Juma’a.

Xi ya bayyana cewa, ya kamata a tabbatar da adalci a duniya, da gina yankin Asiya-Pacific mai zaman lafiya da kwanciyar hankali, kana ya yi kira ga bangarori daban daban su gina makoma ta bai daya ta Asiya-Pacific tare, da kuma samun sabuwar nasara a kan hadin gwiwar yankin.

Xi Jinping ya jadadda cewa, kamata ya yi a tsaya tsayin daka kan bude kofa da gina Asiya-Pacific inda jama’a za su sami wadata tare. Ya ce a shekarar badi, bangaren Sin zai yi tunanin gudanar da dandalin tattaunawar koli na hadin gwiwar duniya kan shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta yadda za a samar da sabon kuzari ga neman ci gaba da samun nasarori a yankin Asiya-Pacific da ma duniya baki daya.

Xi Jinping ya ce, kamata ya yi a tsaya tsayin daka kan samu ci gaba ta hanyar kiyaye muhalli, da gina Asiya-Pacific mai tsabta da kyan gani. Yana mai cewa, bangaren Sin zai bayar da goyon baya don cimma makasudin Bangkok, tare da maraba da kasashen Asiya-Pacific su shiga cikin ajandar ci gaban kasa da kasa.

Har ila yau, Xi Jinping ya bayyana cewa, kamata ya yi a tsaya tsayin daka kan samar da makoma ta bai daya, da gina yankin Asiya-Pacific ta yadda za a rika taimakawa juna. Kuma ya kamata a dage wajen kiyaye manufofin kungiyar APEC, da karfafa huldar abokantaka ta aminci da hakuri da juna da hadin gwiwa da samun nasara tare.

Bugu da kari, ya ce, Sin za ta dade tare da kara bude kofarta ga kasashen waje cikin fage mai fadi da zurfi, da nacewa bin hanyar zamanintarwa iri na kasar Sin, da gina babban sabon tsarin tattalin arziki mai bude kofa, da samar da ci gaba da yayata gogewarta na ci gaba ga duniya musamman ma Asiya-Pacific.(Safiyah Ma)