logo

HAUSA

Sin ta zama misali a fannin inganta ci gaban kasa da kasa

2022-11-18 11:48:55 CMG Hausa

Shugaba Xi Jinping ya bayyana a cikin jawabin da ya bayar a gun taron kolin G20 cewa, kamata ya yi a mai da hankali kan makasudi na dogon lokaci da bukatu masu amfani, ta yadda za a inganta ci gaban kasashen duniya tare. Fitattun mutane daga wasu kasashen duniya sun bayyana cewa, Sin ta zama misali a fannin inganta ci gaban kasa da kasa ta hanyar shawarar “Ziri daya da hanya daya”.

Babban editan jaridar Authority da ake wallafawa a Nijeriya Malachy Uzendu, ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi nasarar kawar da yunwa da fari, ta kuma dade tana amfani da sabbin fasahohin zamani wajen warware matsalolin rashin isashen abinci da fama da bala’in fari, wadanda suke da tsanani matuka ga kasashen Afirka. Don haka, Malachy Uzendu ya ce, jawabin na shugaba Xi Jinping zai ba da kwarin gwiwa ga wasu shugabannin kasashen Afirka.

Shugaban kungiyar raya tattalin arziki da cinikayyar waje ta tarayyar Jamus Michael Sdiumann, ya bayyana cewa, kasar Sin na taimakawa kasashe masu tasowa ta hanyar samar musu da ababen more rayuwa, ita ce manufar da kasar Sin take bi wajen aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”.

Sannan shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa IOC Thomas Bach, ya ce shugaba Xi Jinping na goyon bayan wasannin motsa jiki dake karfafa "hadin kai da hadin gwiwa", kuma muna maraba da jawabinsa matuka. (Safiyah Ma)