logo

HAUSA

Ya Dace Sin Da Afirka Su Bunkasa Hadin Gwiwar Cin Gajiya Daga Fasahohin Amfani Da Makamashi Maras Illa Ga Muhalli

2022-11-17 19:13:38 CMG Hausa

Yayin da hankulan duniya ke kara karkata ga yadda za ta karke a taron COP27, na bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD, masharhanta da dama na ganin taron babbar dama ce ga daukacin masu ruwa da tsaki, ta su hada karfi da karfe wajen lalubo dabarun gaggauwa na shawo kan kalubalen sauyin yanayi, ciki kuwa har da dabarun rage radadin sauyin yanayin, da gano fasahohin jurewa da dorewar rayuwa tare da kalubalen, da rage asarar da sauyin yanayin ka iya haifarwa, da ma batun samar da kudaden gudanar da wadannan ayyuka.

Tuni dai aka yi imanin cewa, nahiyar Afirka na cikin yankunan duniya dake fitar da mafi karancin sinadarai, da iska mai gurbata muhalli a duniya, amma a hannu guda, nahiyar na sahun gaba wajen dandana kuda daga mummunan tasirin sauyin yanayi.

Masharhanta na ganin duba da yadda kasar Sin ke kan gaba, wajen cin gajiya daga fasahohin dakile sauyin yanayi, musamman fannin bunkasa amfani da nau’oin makamashi marasa gurbata muhalli, da wadanda ake iya sabuntawa. Kuma kasar ta jima da kasancewa abokiyar tafiya ga kasashen Afirka a dukkanin fannonin ci gaba, yanzu lokaci yayi da kasashen na Afirka za su fadada koyi daga kasar Sin a wannan fanni.

A cewar Frederick Mutesa, wani kwararre a fannin ilimin samar da ci gaba dan kasar Zambia, kasar Sin ta nunawa duniya kwazon ta a fili wajen bunkasa ci gaba mai dorewa, da raya manufofi na dakile kalubale da matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa. Don haka lokaci ya yi da kasashen Afirka za su gaggauta yin hadin gwiwa da Sin, ta yadda za su yi koyi, da kuma cin gajiyar kwarewar Sin a wannan fanni.

Ko shakka ba bu wannan shawara ce mai kyau, domin kuwa akasarin kasashen nahiyar Afirka na da albarkatu musamman na hasken rana, yayin da a daya bangaren kasar Sin ke da kwarewa, da fasahohin bunkasa samar da makamashi ta hasken rana, wanda hakan ke nuna cewa, idan har sassan biyu sun yi hadin gwiwa, tabbas za a ci babbar gajiya daga makamashi maras gurbata muhalli.

Baya ga fannin raba fasahohi da kasashen Afirka, fannin samar da kudaden dakile tasirin sauyin yanayi, shi ma muhimmin bangare ne da kasashen Afirka za su iya cin gajiya daga Sin, kasancewar dama akwai kyakkyawar dangantaka, da cudanya tsakanin kasashen Afirka da Sin karkashin dandalin FOCAC na bunkasa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da kuma irin tallafi na samar da manyan ababen more rayuwa da kasashen Afirka ke samu daga Sin, karkashin manufofin samar da ci gaba na shawarar ziri daya da hanya daya.

Duk wadannan dalilai, na kara nuna muhimmancin aza kyakkyawan mafari, na ingiza hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin kare muhalli, da bunkasa cin gajiya daga nau’oin makamashi da ake iya sabuntawa.(Saminu Alhassan)