logo

HAUSA

Sin ta dora muhimmanci ga matsalar rashin amfani da yanar gizo

2022-11-17 20:54:06 CMG Hausa

Bisa kididdigar da hukumar kawancen sadarwa ta duniya ta yi, mutane kimanin biliyan 3 a duniya har yanzu ba sa amfani da yanar gizo. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau cewa, Sin ta dora muhimmanci ga matsalar rashin amfani da yanar gizo, inda aka shigar da batun tattalin arzikin yanar gizo karo na farko a cikin ajandar taron kolin kungiyar G20 da aka yi a birnin Hangzhou na kasar. Haka kuma, a yayin taron kolin kungiyar G20 a tsibirin Bali, shugaba Xi Jinping ya sake gabatar da shirin kasar Sin a wannan fanni.

Ta ce Sin tana son zurfafa hadin gwiwa da kasa da kasa wajen kafa tsarin tattalin arzikin yanar gizo na duniya bisa daidaito da amincewa juna, da hadin gwiwa, da samun moriyar juna, da kuma samun wadata tare. (Zainab)