logo

HAUSA

Xi Ya Yi Kira Da Dunkule Tattalin Arzikin Asia Da Pasifik Yayin Da Ake Fuskantar Kalubale

2022-11-17 20:19:39 CMG Hausa

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya bayyana a yau Alhamis cewa, yayin da ake fuskantar sabbin sauye-sauye, akwai bukatar mambobin kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin Asiya da Pasifik wato APEC, su yi waiwaye su dauki darasi daga tarihi, su tunkari kalubalen da ake fuskanta yanzu, tare da jajircewa wajen dunkule tattalin arzikin yankin Asia da Pasifik.

Xi Jinping wanda ya bayyana haka cikin rubutaccen jawabin ga taron kolin shugabannin masana’antu da kasuwanci na kungiyar APEC, ya yi kira da a hada hannu wajen samar da sabbin nasarori a fannin ci gaba da gina al’ummar Asia da Pasifik mai makoma ta bai daya. Ya kuma gabatar da wasu shawarwari 6 game da hakan, wadanda suka hada da, gina tubalin neman ci gaba cikin lumana da daukar dabarun neman ci gaba dake mayar da hankali kan moriyar jama’a da fadada bude kofa ga kasashen waje da jajircewa wajen hadewa da juna da gina nagartaccen tsarin samar da kayayyaki da kuma daukaka aikin raya tattalin arziki.

A cewar shugaba Xi, yankin Asiya da Pasifik ba wuri ne da kowa zai yi abun da ya ga dama ba, kuma bai kamata ya zamo dandalin takara ga manyan kasashe ba. Yana mai cewa, ba za a amince da duk wani yunkuri na tayar da wani yakin cacar baka a yankin ba.

Har ila yau, shugaban na kasar Sin ya bayyana cewa, bin tafarkin neman ci gaba cikin lumana, muhimmin zabi ne da kasarsa ta yi saboda muradun al’ummar Sinawa, kuma za su jajirce ga tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba da hadin gwiwa da samun moriyar juna. Haka kuma, za su mayar da hankali ga kiyaye zaman lafiya da ci gaba a duniya, yayin da suke neman na su ci gaban, kana za su bayar da karin gudunmuwa ga zaman lafiyar duniya da ci gaba, ta hanyar na su ci gaban.

Da yake bayyana bude kofa da dunkulewa wuri guda a matsayin masu muhimmanci ga kwanciyar hankali da ci gaban bil Adama, Xi Jinping ya ce, daukacin al’ummar Asiya da Pasifik ne suka raya yankin ta hanyar hada hannu da shawo kan wahalhalu da kalubale. Yana mai cewa, duk wani yunkuri na kawo tsaiko ko rusa tsarin samar da kayayyaki, da aka samar a yankin cikin shekaru da dama, babu abun da zai haifar face lalata hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin. Ya ce bude kofa zai kawo ci gaba, yayin da rufewa za ta haifar da koma-baya. (Fa’iza Mustapha)