logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya isa Bangkok

2022-11-17 16:46:15 CMG Hausa

Da yammacin yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa filin jiragen saman kasa da kasa na Suvarnabhumi dake Bangkok, fadar mulkin Thailand.

Bisa gayyatar da firaministan masarautar Thailand Prayuth ya yi masa, shugaba Xi Jinping zai halarci taron kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar APEC karo na 29 tare da kai ziyarar aiki a kasar daga ranar 17 zuwa 19 ga watan Nuwamban da muke ciki. (Safiyah Ma)