logo

HAUSA

Sin ya yi maraba da kafuwar babban rukuni mai zaman kansa na harkokin tsaro da ci gaban yankin Sahel

2022-11-17 13:01:06 CMG Hausa

Mataimakin wakilin Sin a MDD Geng Shuang ya bayyana a jiya Laraba cewa, bangaren Sin yana maraba da kafa babban rukuni mai zaman kansa game da harkokin tsaro da ci gaban yankin Sahel. Yana kuma fatan rukunin zai nuna basira wajen tinkarar kalubalolin da yankin ke fuskanta, da fito da manufofi da shawarwarin da suka dace da tsaro da ci gaba.

Geng Shuang ya bayyana a taron bainar jama’a da kwamitin tsaro na MDD ya shirya game da matsalar yankin Sahel cewa, kasar Sin tana goyon baya tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar yankin Sahel, wannan ya sa ta ba da tallafi ga yankuna da kasashe a karkashin wasu tsare-tsare, kamar dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wato FOCAC da shawarar “Ziri daya da hanya daya” da ajandar ci gaban kasa da kasa, ta yadda hakan zai ba da karin gudummawa a kokarin cimma zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a yankin. (Safiyah Ma)