logo

HAUSA

Jihar Lagos ta bullo da alluran riga kafin rotavirus don kare yara daga kamuwa da gudawa

2022-11-17 10:24:55 CMG Hausa

Jihar Lagos dake zama cibiyar tattalin arzikin Najeriya, ta sanya alluran riga kafin rotavirus cikin shirinta na riga kafin yau da kullum ko RI a takaice, domin kare kananan yara ‘yan kasa da shekaru 5 daga kamuwa da zawo ko kuma gudawa.

Jami’ar rigakafin cutar gudawa a ma’aikatar kula da lafiya a matakin farko na jihar (LSPHCB) Taiwo Onoro ce ta bayyana haka ne a Lagos, yayin wani taron wayar da kan jama’a da aka shirya, game da bullo da alluran riga kafin ta rotavirus.

Taiwo ta bayyana cewa, za a fara gangamin riga kafin na tsawon kwanaki 7 a jihar, don ganin an yi wa kowa riga kafin. Daga bisani kuma, za a rika yiwa jama’a riga kafin na rotavirus tare da sauran alluran riga kafin karkahin shirin rigakafi na yau da kullum (RI) da aka tanada a dukkan cibiyoyin lafiya a matakin farko da kuma asibitoci masu zaman kansu dake jihar.(Ibrahim)