logo

HAUSA

Kenya: CMG Ya Shirya Taro Mai Taken “Sin Da Sassan Duniya Sun Kama Sabon Tafarki”

2022-11-17 20:33:48 CMG Hausa

An gudanar da wani taron karawa juna sani tsakanin kafafen watsa labarai na kasar Sin da kasashen Afrika, mai taken “Sin da sassan duniya sun kama sabon tafarki”, wanda reshen babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG a Afrika ya karbi bakuncinsa a birnin Nairobin kasar Kenya jiya.

Shugabannin kafafen watsa labarai da masana da malamai 60, daga kasashe 20, da suka hada da Kenya da Rwanda da Tanzania da Madagascar da Sudan ta Kudu da Zambiya da Saliyo ne suka yi tattaunawa mai zurfi, kan maudu’ai da suka hada da “ Me sabon tafarkin Sin ke nufi ga nahiyar Afrika” da “Ina batun sabon tafarkin gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya” da kuma “Me hadin gwiwa tsakanin kafafen yada labarai na Sin da Afrika zai samar ga al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya”.

Mahalarta taron, sun amince cewa, sabbin ci gaban da kasar Sin ke samu bayan babban taron wakilan JKS karo na 20 zai kawo sabbin damarmaki ga Afrika, haka kuma sabon kuzari ne dake ingiza ginin al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya. Baya ga haka, hadin gwiwa tsakanin kafafen watsa labarai na Sin da Afrika a sabon zamani, na kunshe da dimbin damarmaki. (Fa’iza Mustapha)