logo

HAUSA

Kasar Sin Ba Ta Taba Mantawa Da Aminanta Kasashen Afirka Ba

2022-11-16 17:38:36 CMG Hausa

Yayin da shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 ke can suna tattauna batutuwa dake jan hankalin duniya, kamar farfadowar tattalin arzikin duniya da inganta tsarin kiwon lafiya da batun sauyin yanayi da sauya akala zuwa ga amfani da na’urori na zamani, har ma da batun samar da isasshen abinci da makamashi da makamantansu, a taron kungiyar dake zama na 17 a tsibirin Bali dake kasar Indonesia.

Kungiyar G20 da aka kafa a shekarar 1999, ta zama wani muhimmin dandalin hadin gwiwar kasashen duniya a fannin raya hada-hadar kudade da tattalin arziki. Kuma yanzu haka tana da kasashe mambobi 19 gami da kungiyar tarayyar Turai (EU).

A yayin da bangarorin kasa da kasa ke fatan ganin manyan kasashe masu sukuni za su karfafa tsarin gudanarwa a fannin manufofin cudanyar bangaori daban-daban da kara bude kofa da tafiya tare da kowa da hadin gwiwar moriyar bai daya, shi kuwa shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya bayyana goyon bayan shigar da kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ne a cikin kungiyar ta G20.

Wannan batu da shugaba Xi ya gabatar ya kara tabbatar da cewa, kasashen Sin da Afirka sun zama abin da Malam Bahaushe ke cewa, “’yan uwa rabin jiki”. Kuma a duk lokacin da bangaren Sin ya ga abin da zai shafi moriyar kasashen Afirka musamman kasashen masu tasowa, ya kan yi kokarin nusar da duniya bukatar kare muradunsu tare da mara musu baya, wajen ganin an cimma burin da ake fata, matakin dake kara jaddada sahihancin hadin gwiwar sassan biyu.

Sanin kowa ne cewa, kasashen duniya musamman masu tasowa, wanda kasashen Afirka ke ciki, suna fuskantar kalubale na koma bayan tattalin arziki. Wannan ne ma ya sa shugaba Xi ya gabatar da shawarar kafa dangantakar abokantakar neman farfado da tattalin arziki da dora muhimmanci ga aikin neman ci gaba da raya al’umma. Sabanin yadda wasu kasashe ke neman kafa kansa ba tare da la’akari da ragowar kasashe ba, wai kowa ya kar kifi gorarsa. Shi kuwa shugaba Xi, cewa ya yi, ya dace irin wadannan kasashe su taimakawa sauran kasashe, da ba su karin damammakin da suke bukata. Wato ka so wa dan uwanka, abin da kake so a kanka.

Baya ga kayayyakin more rayuwa da kasashen Afirka suka amfana da su karkashin hadin gwiwar sassan biyu, wato Sin da Afirka. Daga lokaci zuwa lokaci ko dai a taruka ko dandalolin kasa da kasa, bangaren Sin kan yi kokarin kare muradun kasashe masu tasowa baki daya. Kasar Sin ba ta taba mantawa da aminanta kasashe Afirka ba. Abin da ke kara tabbatar da sahihancin alakar sassan biyu. (Ibrahim Yaya)