logo

HAUSA

Ya kamata kasashen Sin da Amurka su cimma daidaitaciyyar alkibla ta bunkasa alakarsu

2022-11-16 09:40:26 CMG Hausa

Ganawar da shugaba Xi Jinping na Sin da takwaransa na Amurka Joe Biden suka yi, yayin taron kolin G20 a tsibitin Bali na kasar Indonesiya, ta zamo babbar dama ga kasashen biyu, ta tattauna muhimman batutuwa da suke jan hankalinsu.

Tum ma kafin wannan ganawa, masharhanta na ganin hakan zai zamo wata dama, ta tattaunawa, da warware banbance-banbance tsakanin jagororin manyan kasashen biyu, tare da bitar matsayar kasashen game da muhimman batutuwa. 

A iya cewa, akwai alamun nasara a wannan ganawa, duba da yadda jagororin biyu suka amince da bukatar kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen su, ta bin hanyoyi mafiya dacewa na warware sabani, da inganta tattaunar jami’ai cikin hadin gwiwa.

Cikin muhimman batutuwa da ke jan hankalin sassan biyu, akwai batun yankin Taiwan na kasar Sin. Kuma a wannan karo shugaban Amurka Joe Biden ya sake jaddada cewa, kasar sa na nan kan matsayin ta, na amincewa da manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, da sanarwa 3, na hadin gwiwar da sassan biyu suka amincewa, baya ga batun kaucewa gurgunta yanayin zaman lafiyar lardin na Taiwan. 

Kaza lika kamalan shugaba Biden, cewa Amurka ba ta da burin ganin ta dakile ci gaban kasar Sin suna da ma’anar gaske, duba da cewa hakan na cikin batutuwa da aka jima ana fatan warware su tsakanin sassan 2.

Sanin kowa ne cewa, Sin da Amurka, na kan gaba wajen shigar da babban karfi na farfado da tattalin arziki duniya, da ingiza hadin gwiwa a fannoni daban daban, wanda hakan ke zaburar da bunkasuwar rayuwar daukacin bil adama, kuma hakan manufa ce da ke shafar moriyar daukacin bil adama, ciki har da kasashe masu tasowa. 

Lura da moriyar dake tattare da hadin gwiwar Sin da Amurka ga su kasashen 2, da ma duniya baki daya. Al’ummun duniya na kara maida hankali kan hadin kan sassan, tare da fatan ganin sun cimma matsaya da za ta yi jagora ga cin moriyar juna, tare da fatan “gudu tare a tsira tare”. (Saminu Hassan, Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)