logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Ba Da Amsarta Kan Yadda Ake Raya Duniya

2022-11-16 21:10:55 CMG Hausa

Yau da yamma aka rufe taron kolin kungiyar G20 karo na 17 a tsibirin Bali na kasar Indonesia. A yayin taron, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi muhimmin jawabi, inda ya bayar da muhimmanci kan batun ci gaba. Ya nuna cewa, wajibi ne kasashe mambobin kungiyar G20 su kara azama kan raya duniya mai juriya da kowa zai mora da cin gajiya. Kuma shawararsa ta samu amincewar sassa daban daban. Ana ganin cewa, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawara mai muhimmanci a lokaci mafi dacewa, wadda za ta kara kuzari kan ci gaban duniya mai dorewa, ta kuma nuna hikimar kasar Sin kan amsa tambayoyi guda 2, wato me ya faru a duniya? Me za mu yi a nan gaba?

Ta yaya za a kara azama kan raya duniya da ya kunshi kowa? Kamata ya yi kasashen duniya su girmama juna, su nemi samun daidaito duk da kasacewar bambanci a tsakaninsu, su yi zaman tare cikin lumana, kana su kara azama kan raya tattalin arzikin duniya da ke bude kofa ga kowa, a maimakon mayar da wasu saniyar ware. Ta yaya za a raya duniya da kowa zai ci gajiya? Kamata ya yi kasashen da ke kan gaba a duniya su taimakawa sauran kasashe da zuciya daya domin samun ci gaba na bai daya, kamar yadda kasar Sin take yi kullum. Shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin na mara wa kungiyar AU baya wajen shiga kungiyar G20, wanda a ganin wani masanin kasar Kenya kan al’amuran duniya, hakan zai sanya kasashen duniya su kara mai da hankali kan kasashe masu tasowa, da kara karfin kasashe masu tasowa na bayyana ra’ayoyinsu a tsare-tsaren cudanyar sassa daban daban. (Tasallah Yuan)