logo

HAUSA

Kamfanoni fiye da 5600 sun halarci bikin CHTF karo na 24

2022-11-16 13:45:01 CMG Hausa

An bude bikin baje kolin manyan na’urorin zamani na duniya na Sin karo na 24 a Shenzhen jiya Talata. Fadin yankin bikin da za a shafe kwanaki 5 ana gudanarwa ya kai sama da muraba’in mita dubu 300, wanda ya ja hankalin masu baje koli fiye da 5600 daga kasashe da yankuna 41 da kayayyaki fiye da 8600. Jigon bikin shi ne “Gyare-gyare a fannin kimiyya da fasaha sun inganta kirkire- kirkire, kirkire-kirkiren kimiya sun ingiza bunkasuwa ”.

A yayin bikin, a rumfar da ma’aikatar cinikayyar Sin ta kafa musamman, an nuna nasarorin da kasar Sin ta samu, wajen gina tsarin tattalin arziki mai salon bude kofa, da samar da sabbin damammaki a hadin gwiwar tattalin arzikin kasa da kasa, da yin takara ta hanyar yin gyare-gyare da inganta cinikayyar ketare. Baje kolin na musamman na kasar Sin, ya kunshi dandalin Intanet na abubuwa, da fasagar 5G “Smart+” da ragowar fasahohi da nasarorin masu nasaba.

Ma’aikatar aikin gona da raya yankunan karkara ta kasar Sin, ta mayar da hankali wajen nuna nasarorin da aka cimma a bangaren kimiya da fasaha da fasahar aikin gona ba tare da gurbata muhalli ba. Bikin na bana ya shirya baje kolin nasarorin da aka cimma a fannin fasahohin zamani na tsimin ruwa a karon farko, da shirya taron kirkira hanyoyin tsimin ruwana kasar Sin a karo na farko. (Safiyah Ma)