logo

HAUSA

Masana: Hadin gwiwar Sin da Afirka na kara karfin Afirka a fannin aikin Injiniya

2022-11-16 13:50:40 CMG Hausa

Kwararru a nahiyar Afirka sun bayyana cewa, cudanya tsakanin al’ummun Afirka da Sinawa, yana kara ci gaban nahiyar a fannin aikin injiniya, baya ga gagarumar gudummawa da alakar ke bayarwa ga bunkasuwar zamantakewar al’umma da tattalin arzikin nahiyar.

Shugaban kungiyar injiniyoyi ta Afirka (FAEO) Carlien Bou-Chedid ne ya bayyana hakan, yayin wata zantawa a baya-bayan nan da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Yana mai cewa, kasar Sin ta gudanar da ayyuka da dama a Afirka, wadanda kuma suka taimakawa nahiyar koyon darussa masu tarin yawa daga gare su.

Shugaban kungiyar ya jaddada cewa, bangaren aikin injiniya na Afirka na fuskantar kalubale daban-daban, wadanda ke bukatar kulawa, domin cike gibin dake akwai a fannin kwararrun ma’aikata, da fasahohi da kuma matsaloli na kudade.

Kan wannan batu ne, Bou-Chedid, ya zayyana nasarorin da kasar Sin da cimma a fannin Ilimi da kokarin raba kwarewarta, don baiwa injiniyoyin Afirka damar koyon sabbin fasahohi na zamani a fannonin aikin injiniya, ta yadda za su zage damtse a kokarin da nahiyar ke yi na neman ci gaba. (Ibrahim)