logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da ministan harkokin wajen Rasha

2022-11-16 13:03:20 CMG Hausa

Mamban hukumar siyasa na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin kuma mamban majalisar gudanarwar kasar, Wang Yi ya gana da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov a tsibirin Bali jiya Talata agogon wurin.

Lavrov ya bayyana cewa, sake zabar Xi Jinping a matsayin babban sakataren kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin ba tare da wata hamayya ba, ya nuna kimarsa a siyasa da yarda da goyon bayan da jama’ar kasar Sin ke nuna masa.

Bangaren Rasha yana fatan inganta mu’ammala tsakanin manyan jami’an kasashen biyu zuwa babban matsayi, da kara tabbatar da hadin gwiwa bisa manyan tsare tsare tsakanin Rasha da Sin.

Wang Yi ya bayyana cewa, abubuwa hudu da ya kamata mu yi” da “abubuwa hudu da suka dace mu yi tare ” da shugaba Xi Jinping ya gabatar, su ne hanyoyin da bangaren Sin ya bi wajen daidaita matsalar Ukraine. Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan matsayi na nuna adalci, da taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da tattaunawar zaman lafiya. A nasa bangare Lavrov ya bayyana cewa, har kullum kofar bangaren Rasha a bude take, na yin sulhu da tattaunawa.(Safiyah Ma)