logo

HAUSA

Kamfanin Huawei zai taimaka wajen habaka ci gaban fasahar ICT a Angola

2022-11-16 13:55:32 CMG Hausa

Katafaren kamfanin fasahar sadarwa na kasar Sin wato Huawei, ya kaddamar da wani rukunin masana’antun fasahar sadarwa a Angola, wanda ake sa ran zai taimaka wajen horas da masu hazaka na cikin gida a bangaren fasahar sadarwar zamani (ICT) da hanzarta zamanintar da bangaren a kasar dake kudancin Afirka.

A yayin bikin kaddamarwar da ya gudana a Luanda, babban birnin kasar, an kuma sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna, tsakanin kamfanin Huawei da ma’aikatar sadarwa da fasahohin zamani da jin dadin jama’a ta kasar, inda kamfanin na kasar Sin zai horas da kwararru fiye da dubu 10 a fannin fasahar sadarwa na kasar nan da shekaru 5 dake tafe.

Kamfanin Huawei ya bayyana cewa, zai samar da kayayyakin koyarwa ga cibiyoyin ilimi na kasar, baya ga shirin bayar da tallafin karatu ga daliban da suka yi fice, da shehunan malamai da kuma cibiyoyi.

A jawabinsa, ministan sadarwa da fasahar sadarwa da walwalar jama’a na kasar, Mario Oliveira, ya bayyana a yayin bikin cewa, rukunin masana’antun, zai taimaka wajen bunkasa fasahar sadarwar kasar, da ba da damar samun horo bisa mizanan kasa da kasa, ba kawai ga ’yan Angola kadai ba, har ma da kwararru daga wasu kasashen Afirka. (Ibrahim Yaya)