logo

HAUSA

Yawan Kayayyakin Da Masana’antu Sin Suka Samar Ya Karu Da Kaso 5 A Watan Oktoba

2022-11-15 19:33:47 CMG Hausa

Yawan kayayyakin da masana’antu kasar Sin suka samar, wanda muhimmin ma’auni ne na tattalin arziki, ya karu da kaso 5 a watan Oktoban bana.

Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar ta fitar a yau Talata, sun nuna cewa, an samu saurin karuwar da kaso 0.2 fiya da na rubu’i na 3.

Bangaren sayayyar kayayyakin yau da kullum ya karu da kaso 0.6 cikin watanni 10 na farkon bana, inda jimilar adadin sayayyar kayayyakin ya kai kimanin yuan triliyan 36.05, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 5.11.

Jarin da Sin ta zuba kan kadarori kuma, ya karu da kaso 5.8 a watannin 10 na farkon bana, inda jarin da take zubawa a masana’antun fasahohin zamani ke ci gaba da karuwa. (Fa’iza Mustapha)